logo

HAUSA

Xi Jinping ya gana da Michelle Bachelet

2022-05-25 14:57:16 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da babbar jami'ar hukumar MDD mai lura da kare hakkokin bil adama Michelle Bachelet ta kafar bidiyo a yau Laraba a nan birnin Beijing.

A yayin ganawar, Xi Jinping ya yi maraba da ziyarar Bachelet a kasar Sin, kuma ya nuna cewa, kasar Sin tana son aiwatar da shawarwari, da hadin gwiwa tare da dukkan sassan duniya bisa daidaito da mutunta juna, don sa kaimi ga bunkasuwar ayyukan kare hakkin bil'adama na kasa da kasa, tare da amfanar jama'ar kasashe daban daban.

A cewarsa, yanzu haka abu mafi mahimmanci shi ne a yi abubuwa guda hudu yadda ya kamata. Na daya shi ne riko da tsarin da ya shafi mutane, wato mayar da al’umma gaban komai. Na biyu mutunta hanyar ci gaban 'yancin dan Adam na kowace kasa. Na uku yin la'akari da kowane irin hakki na dan adam. Na hudu, karfafa tsarin kula da hakkin dan Adam na duniya.

A nata bangaren, Bachelet ta ce, za ta yi mu'amala kai tsaye sosai tare da gwamnatin kasar Sin, da masu aiki a sassa daban daban na kasar. Ta kuma bayyana imanin cewa, wannan ziyara za ta taimaka mata wajen kara fahimtar kasar Sin sosai. Ta ce hukumarta na son karfafa cudanya da bangaren kasar Sin, da tattauna da hadin gwiwa, kana da yin kokari tare, don sa kaimi ga ci gaban ayyukan kare hakkin bil'adama na duniya. (Mai fassara: Bilkisu Xin)