logo

HAUSA

MDD ta yi Allah wadai da harin da kungiyar M23 ta kaddamar kan dakarun wanzar da zaman lafiya a Kongo

2022-05-25 11:21:03 CMG Hausa

Kwamitin sulhun MDD ya yi Allah wadai da babbar murya da harin da mayakan ’yan tawayen M23 suka kaddamar kan dakarun kiyaye zaman lafiya na MDD, da sojojin jamhuriyar demokradiyyar Kongo a garin Shangi dake lardin arewacin Kivu.

A sanarwar da aka rabawa manema labarai, mambobin kwamitin sulhun sun jaddada aniyarsu na yin Allah wadai da dukkan hare-hare da tsokanar da ’yan tawayen ke kaddamarwa kan dakarun kiyaye zaman lafiyar MDDr a Kongo da aka fi sani da MONUSCO. Sun bayyana cewa, hare-haren da ake shiryawa da kuma kaddamarwa kan dakarun kiyaye zaman lafiya zai iya kasancewa a matsayin laifukan yaki karkashin dokokin kasa da kasa. Don haka, sun bukaci hukumomin a Kongon da su gaggauta bincike kan wadannan hare-hare, kana su kamo dukkan masu ruwa da tsaki don gurfanar da su a gaban shari’a, sannan su ci gaba da samar da muhimman bayanai dangane da irin nasarorin da ake samu a ayyukan kiyaye zaman lafiya ga kasashen da suke bayar da gudunmawar dakarun tsaronsu. (Ahmad Fagam)