logo

HAUSA

MDD ta bukaci bangarori a Sudan su gaggauta samar da mafita ga matsalar siyasar kasar

2022-05-25 14:53:07 CMG Hausa

Babban jami’in MDD ya yi kira ga bangarori a kasar Sudan, su gaggauta lalubo hanyar warware matsalar da kasar take ciki.

Wakilin musamman na babban sakataren MDD, kuma shugaban shirin majalisar na taimakawa mika mulki a Sudan, Volker Perthes ya ce, yanayin na Sudan na cikin hadari ta fuskoki daban-daban, ciki har da siyasar kasar da yanayin zaman takewa da na tattalin arziki. Ya ce lokacin cimma maslahar siyasa domin samun mafita na kurewa kasar.

A cewarsa, yunkurin hukumomi 3 da suka hada da MDD da Tarayyar Afrika da kungiyar raya gabashin Afrika ta IGAD domin saukaka tattaunawa tsakanin bangarorin kasar na bukatar kyakkaywan yanayi kafin ya cimma nasara. Ya kara da cewa, dabara ta ragewa Sudan, musammam hukumomi, na samar da wannan yanayin. (Fa’iza Mustapha)