logo

HAUSA

Shugaba Xi ya amsa wasikar da Sarah Randy ta rubuta masa

2022-05-24 20:01:54 CMG Hausa

Kwanan nan ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya amsa wasikar da Madam Sarah Randy, wata kawa daga Iowa ta kasar Amurka ta rubuta masa.

A cikin wasikar, Xi Jinping ya bayyana cewa, al'ummomin kasashen Sin da Amurka muhimman mutane ne, kuma zumuncin dake tsakanin al'ummomin kasashen biyu ba wai kawai wata aba ce mai kima ba, har ma ta samar da wani muhimmin tushe na raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. (Ibrahim)