logo

HAUSA

Kasar Sin na adawa da siyasantar da ci gaban kimiyya

2022-05-24 16:07:27 CMG Hausa

Zaunannen wakilin Sin a MDD Zhang Jun, ya ce kasarsa na adawa da yadda wasu gwamnatoci ke siyasantar da batutuwan da suka shafi ci gaban fasaha da kokarin dankwafe kamfanonin fasaha na wasu kasashe.

Zhang Jun ya ce duniyar kimiyya ba fage ne da wata kasa za ta ci nasara daga faduwar wata ba. Haka kuma, bai kamata a ce wata kasa daya tilo ce za ta kasance kan gaba wajen kirkire-kirkiren fasaha ba. (Fa’iza)