logo

HAUSA

Rahoton CNN ya ci mutuncin tawagar kasar Sin a taron tattalin arziki na duniya

2022-05-24 11:25:07 CMG Hausa

Tawagar kasar Sin a babban taron tattalin arzikin duniya na bana, ta ce kafar yada labarai ta CNN, ta ci mutuncinsu cikin rahotonta kan shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky.

Cikin rahoton nata, CNN ta ruwaito wani dan siyasar Amurka na cewa, bayan shugaba Zelensky ya kammala gabatar da jawabi ta kafar bidiyo yayin taron na Davos, jami’an tawagar kasar Sin ba su tashi sun tafa masa kamar yadda sauran mahalarta taron suka yi ba, maimakon haka, sai suka fice daga dakin taron.

Tawagar ta kasar Sin ta ce babu kanshin gaskiya cikin rahoton na CNN. Jami’an sun shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, suna tattaunawa da shugabar hukumar kula da makamashi ta duniya, Fatih Birol, a lokacin da Volodymyr Zelensky ya gabatar da jawabinsa. (Fa’iza Mustapha)