logo

HAUSA

Masanin Zambiya: Takunkumin kasashen yamma na haifar da illa ga tattalin arzikin duniya

2022-05-24 15:58:52 CMG Hausa

Kwanan nan ne a yayin da yake zantawa da kafar CMG, shahararren masanin siyasa na kasar Zambiya, Neo Simutanyi ya ce, Rasha, babbar kasa ce dake fitar da alkama da makamashi, kuma irin takunkuman da Amurka da sauran wasu kasashen yammacin duniya suka sanya mata, sun riga sun haifar da mummunar illa ga tattalin arziki da rayuwar al’ummar duk duniya.

Mista Simutanyi ya bayyana cewa, duba da takunkuman da aka kakkaba mata, Rasha ta kasa halartar harkokin kasuwancin kasa da kasa, kana, ba za ta iya fitar da wasu manyan hajojinta zuwa kasuwannin duniya ba. Rikicin Rasha da Ukraine ya kawo mummunar illa ga tattalin arzikin duniya. (Murtala Zhang)