logo

HAUSA

Wang Yi ya zanta da Michelle Bachelet a birnin Guangzhou

2022-05-24 10:41:21 CMG Hausa

Babban dan majalissar gudanarwa, kuma ministan wajen kasar Sin Wang Yi, ya gana da babbar jami’ar hukumar MDD mai lura da kare hakkokin bil adama Michelle Bachelet a birnin Guangzhou na kasar Sin.

Yayin ganawar tasu a jiya Litinin, Wang Yi ya jaddada cewa, har kullum JKS na sanya bukatun al’ummar kasa gaban komai, kuma jam’iyyar na jagorantar al’ummar Sin bisa tsarin mulkin gurguzu mai halayyar musamman, wanda ya dace da yanayin kasar, ta kuma cimma manyan nasarori a tarihi, masu alaka da aiwatar da sauye sauye da bude kofa ga ketare, matakin da ya yi matukar samun karbuwa tsakanin al’ummar kasar.

Wang ya kara da cewa, har kullum kasar Sin na dora muhimmanci ga damar al’umma na samun ci gaba, da kare ’yancin bil adama na al’ummar kasar bisa doka, da kare ’yancin kananan kabilun kasar.

Kaza lika Sin na ingiza burin gina al’umma mai makomar bai daya ga dukkanin bil adama, tana kuma bayar da gudummawarta wajen warware manyan kalubalolin dake addabar bil adama, tana ingiza ci gaban manufofin kare hakkin bil adama a sassan duniya baki daya.

A nata bangare kuwa, Bachelet ta taya kasar Sin murnar cimma manyan nasarori a fannonin bunkasar tattalin arziki da zamantakewar al’umma, tare da kwazonta na goyon baya da kare hakkokin bil adama.

Jami’ar ta ce hukumar MDD mai lura da kare hakkokin bil adama ko OHCHR, na maida hankali matuka ga rawar da Sin ke takawa, tana kuma fatan amfani da wannan ziyara da take yi a Sin, a matsayin wata dama ta kara kyautata fahimtar juna da yarda, da zakulo dabarun shawo kan manyan kalubalolin dake addabar duniya, da kuma ingiza ci gaban manufofin kare hakkin bil adama a matakin kasa da kasa. (Saminu)