logo

HAUSA

MDD ta yi kira da a shawo kan matsalar rashin abinci a duniya

2022-05-24 10:29:59 CMG Hausa

Babban zauren MDD, ya amince da wani kudurin da ya yi kira ga kasa da kasa, su yi kokarin shawo kan matsalar rashin abinci da ake fuskanta a duniya.

Kudurin wanda aka amince da shi a jiya, ya yi kira ga kasashen duniya su gaggauta taimakawa kasashen da matsalar abinci ta shafa, ta hanyar hada hannu wajen daukar matakan da suka hada da, samar da taimakon abinci na gaggawa da shirye-shiryen samar da abincin da taimakon kudi da karawa da bazakomar dabarun samar da abinci.

Ya kuma yi kira da inganta tsarin cinikayya tsakanin kasa da kasa na bai daya, bisa doka da daidaito, karkashin jagorancin hukumar kula da cinikayya ta duniya WTO.

Har ila yau, kudurin ya yi kira da kasa da kasa ciki har da na kugiyar G7 da ta G20, su sanya batun wadatar abinci kan gaba cikin ajandunsu, tare da taimakawa kokarin al’ummun duniya na lalubo bakin zaren matsalar. (Fa’iza Mustapha)