logo

HAUSA

Sin ta fitar da sabon rumbun bayanai mai kunshe da karin nau’o’in halittu masu rai

2022-05-23 10:50:11 CMG Hausa

A cewar cibiyar nazarin kimiyya ta kasar Sin CAS, kasar ta fitar da sabon rumbun bayanai, mai kunshe da jerin sabbin halittu, domin kiyaye bayanai game da nau’o’in halittu daban daban.

Kundin na bana mai suna “Catalogue of Life China 2022 Annual Checklist” a Turance, na kunshe da sabbin nau’o’in halittu masu rai 10,343, kari kan na shekarar 2021. Da wannan kari, yanzu haka jerin halittun dake cikin kundin sun kai 138,293, ciki har da dabbobi 68,172, da tsirrai 46,725, da nau’o’in fungi 17,173 da dai sauran su.

A cewar wani jami’i mai aiki da wani kwamitin dake karkashin cibiyar CAS, wannan kundi na samar da bayanai masu amfani ga masu binciken nau’o’in halittu masu rai, da masu tsara manufofin kare muhallin halittu, kuma Sin ita ce kasa daya tilo a duniya, wadda a duk shekara ke wallafa jadawalin nau’o’in halittu masu rai.

Sassan dake hadin gwiwar fitar da wannan kundi sun hada da masu bincike na cibiyar nazarin dabbobi, da takwararta ta nazarin tsirrai, da cibiyar nazarin kananan halittu masu rai, da cibiyar nazarin halittu masu rai ta Chengdu, da kuma cibiyar nazarin teku dake karkashin CAS, da sauran wasu karin cibiyoyin. (Saminu)