logo

HAUSA

Taron kolin kwamitin lafiya na MDD zai mayar da hankali kan yaki da COVID-19 da kiwon lafiya don zaman lafiya

2022-05-23 11:24:31 CMG Hausa

Taron kolin kwamitin kiwon lafiya na MDD, WHA karo na 75, wanda aka bude a ranar Lahadi a birnin Geneva na kasar Switzerland, zai mayar da hankali kan manyan batutuwa da suka hada da batun ci gaba da tinkarar yaki da annobar COVID-19, da batun kula da sha’anin kiwon lafiyar kasa da kasa don samun zaman lafiya.

Annobar COVID-19 ta kasance a matsayin muhimmin batu da taron WHA na wannan shekarar zai ba da muhimmanci kanta, wanda shi ne irinsa na farko da aka gudanar a Geneva kuma ya samu halartar wakilai a zahiri tun bayan barkewar annobar sama da shekaru biyu da suka gabata.

Ko da yake, alkaluman hukumar lafiya ta duniya WHO sun nuna cewa, adadin masu kamuwa da cutar COVID-19 ya yi matukar raguwa, tun bayan da cutar nau’in Omicron ta kai matsayin koli a watan Janairun wannan shekara, kuma adadin mutanen da ke mutuwa ya kasance mafi karanci tun a watan Maris na shekarar 2020, babban daraktan hukumar WHO, Dr. Tedros Adhanom Ghebreyesus a jawabin da ya gabatar na bude taron WHA ya jaddada cewa, har yanzu annobar ba ta kare ba, sannan cutar ba za ta taba karewa ba har sai ta kare a dukkan sauran sassa na duniya.

Ya bukaci dukkan kasashe da su maida hankali wajen cimma nasarar gudanar da kashi 70 bisa 100 na riga-kafin cutar nan ba da jimawa ba, sannan a ba da fifiko wajen yiwa dukkan ma’aikatan kiwon lafiya riga-kafin, da kuma mutanen da shekarunsu na haihuwa ya zarce 60 da dukkan mutanen dake da barazanar kamuwa da cutar. (Ahmad)