logo

HAUSA

Shugaban Zimbabwe ya kare jarin da Sin take zubawa a Afirka

2022-05-23 19:33:35 CMG Hausa

Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, ya yabawa masu zuba jari na kasar Sin kan yadda suka sauya yanayin tattalin arzikin kasarsa da ma sauran sassan Afirka, yayin da yake caccakar kasashen yammacin duniya, kan yadda suka wawushe albarkatun Afirka tsawon shekaru da dama.

A cikin bayaninsa na mako-mako da ake wallafawa a jaridar The Sunday Mail mallakin gwamnati, Mnangagwa ya ce, duk da shigar jarin da kasar Sin take zubawa a nahiyar Afirka a nakare, hakan ya haifar da da mai ido cikin kankanin lokaci. (Ibrahim)