logo

HAUSA

Masu sayayya na kara gamsuwa da hidimar kai kayayyaki gida a kasar Sin

2022-05-23 13:54:21 CMG Hausa

Alkaluman nazari sun nuna cewa, cikin rubu’in farko na bana, masu sayayya sun kara nuna gamsuwa da hidimar kai kyayyaki gida ta kasar Sin.

Bisa nazarin ofishin kula da aika sakonni na kasar Sin, a cikin rubu’in na farkon bana, alkaluman auna gamsuwar masu sayayya ya kai maki 80, wanda ya karu da maki 1.2 akan na bara.

Alkaluman a yankunan Shaanxi da Ningxia da Beijing da Liaoning da Sichuan da kuma Shandong, sun kai maki 80, lamarin da ke nuna kyautatuwar hidimar a lardunan.

Ofishin ya kara da cewa a kan kammala kai kaso 69.4 na sakonni cikin sa’o’i 72 a tsakaninn yankunan kasar, sai dai sake bullar annobar COVID-19 a lokacin, ya sa adadi raguwa da kaso 2.83. (Fa’iza Musapha)