logo

HAUSA

Shugabar hukumar kare hakkin dan Adam ta MDD ta iso kasar Sin domin ziyarar aiki

2022-05-23 19:31:31 CMG Hausa

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana cewa, shugabar hukumar kare hakkin bil'adama ta MDD Michelle Bachelet ta iso kasar Sin Litinin din 23 ga watan Mayu.

A yayin da take kasar ta Sin, Bachelet za ta ziyarci lardin Guangdong da ke kudancin kasar, da yankin Xinjiang na Uygur mai cin gashin kansa dake arewa maso yammacin kasar Sin, kana za ta yi tattaunawa mai zurfi da jama'a daga dukkan bangarori na al'umma. (Ibrahim)