logo

HAUSA

Wani harin kwantar bauna ya yi sanadin rayukan ’yan aware 4 a Kamaru

2022-05-23 10:29:59 CMG Hausa

Rundunar sojin Kamaru ta ce, a kalla ’yan aware 4 aka kashe yayin fafatawarsu da dakarun gwamnati, a yankin kudu maso yammacin kasar mai fama da rikici, sanadiyyar kwantar baunar da ’yan awaren suka yi wa dakarun.

’Yan aware da dama sun ji rauni yayin da dakarun suka dakile kwantar baunar a yankin Otou dake kusa da iyakar kasar da Nijeria. Rundunar ta kara da cewa, sojojinta biyu sun ji rauni yayin fafatawar.

A makon da ya gabata ne, ’yan awaren suka bayyana a shafin sada zumunta cewa, sun yanke shawarar toshe hanyar da ta hada Kamaru da Nigeria a yankin, inda suka yi barazanar farwa sojoji da fararen hular da suka yi yunkurin bin hanyar.

Tun daga shekarar 2017, dakarun gwamnati ke yaki da ’yan aware a yankunan arewa maso yammaci da kudu maso yammacin kasar, wadanda ke da rinjayen masu amfani da harshen Ingilishi. (Fa’iza Mustapha)