logo

HAUSA

Sin: Manufar kasar Sin daya tak a duniya ita ce tsarin da al’ummomin kasa da kasa suka aminta

2022-05-23 19:16:25 CMG Hausa

 

Babban zaunen majalisar kiwon lafiya na duniya karo na 75, ya yanke shawarar yin watsi da shawarar da kasashe daban-daban suka gabatar, na gayyatar Taiwan zuwa taron majalisar lafiya ta duniya. Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a taron manema labaru da aka saba shiryawa Litinin din nan cewa, wannan ya nuna karara cewa, manufar kasar Sin daya tilo a duniya, ita ce tsarin da al'ummomin kasa da kasa suka aminta da shi, kuma ba za a iya kalubalantarsa ba.

Wang Wenbin ya kuma amsa tambayar da wani dan jarida ya yi masa kan kaddamar da "Tsarin tattalin arzikin kasashen dake yankin tekun Indiya da Fasifik" da shugaban Amurka ya sanar a ziyarar da ya kai a Asiya. Ya bayyana cewa, kasar Sin kamar sauran kasashen yankin Asiya da tekun Fasifik, tana farin cikin ganin shirye-shiryen da suka dace wajen karfafa hadin gwiwarsu, amma tana adawa da yunkurin haifar da rarrabuwar kawuna, da yin fito na fito.

Ya kuma ce, batun Taiwan da na Ukraine batutuwa ne daban-daban guda biyu, kuma bai dace a kwatanta batutuwan guda biyu ba. (Ibrahim)