logo

HAUSA

Wang Yi: Manufar Amurka ta hadin gwiwar tekun Indiya da Pacific ba za ta yi nasara ba

2022-05-22 20:51:38 CMG Hausa

A yau Lahadi, 22 ga watan Mayu, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar, Wang Yi, tare da ministan harkokin wajen kasar Pakistan, Bilawal Zardari, sun gudanar da taron ‘yan jaridu na hadin gwiwa bayan tattaunawarsu.

Da yake amsa tambayoyin ‘yan jaridu game da abin da ake kira wai “dabarun hadin gwiwar kasashen yankunan tekun Indiya da Pacific” wato "Indo-Pacific strategy" a Turance, wanda kasar Amurka ke fadi-tashin ganin ta dakile tasirin kasar Sin, Wang Yi ya ce, wannan manufa ta "Indo-Pacific strategy" da Amurka ke hankoron kafawa tana janyo hankali da kuma karin damuwa a duniya, musamman a kasashen dake yankunan tekun Asiya da Pacific.

Gaskiya dai za ta yi halinta, cewa wannan manufar “hadin gwiwar kasashen yankunan tekun Indiya da Pacific”, dabarun ne da ake amfani da su wajen haifar da baraka da kawo tarnaki ga zaman lafiya, daga karshe manufar ba za ta kai ga cimma nasara ba. (Ahmad)