logo

HAUSA

Cinikin wajen kasar Sin ya samu ci gaba cikin sauri

2022-05-22 16:05:52 CMG Hausa

Alkaluman babbar hukumar kwastam ta kasar Sin sun nuna cewa, kasar Sin ta kasance kasa mafi girma ta cinikin kayayyaki a shekarar 2013, daga baya adadin cinikin kayayyaki da cinikin ba da hidima na kasar sun kai sahun gaba a duniya a shekarar 2020, ana iya cewa, cinikin wajen kasar Sin ya samu ci gaba cikin sauri.

A cikin shekaru goma da suka gabata, adadin kamfanonin dake gudanar da cinikin waje da kasar Sin ya karu da ninki 1.7, ban da abokan ciniki na gargajiya kamar su kungiyar tarayyar Turai EU, da kasashen Amurka da Japan da Koriya ta Kudu, kasar Sin tana yin kokari matuka, domin kara habaka cinikin dake tsakaninta da kasashe mambobin kungiyar ASEAN, da kasashen nahiyar Afirka, da kuma Latin Amurka, wadanda suka fi saurin ci gaban tattalin arziki. Abu mafi faranta rai shi ne, adadin cinikin wajen da kasar Sin ta gudanar da kasashen da suka shiga shawarar ziri daya da hanya daya ya kai kaso 29.7 bisa dari, kwatankwancin adadin cinikin wajen kasar ta Sin.

A halin da ake ciki yanzu, cinikin wajen yana fama da matsala sakamakon sauye-sauyen yanayin cikin gidan kasar Sin da na kasa da kasa, game da hakan mataimakin ministan kasuwancin kasar Sin Sheng Qiuping ya bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da nacewa kan manufar bunkasa cinikin waje mai inganci sannu da hankali, domin samar da hidima ga sabon tsarin ci gaban kasar da aka tsara. (Jamila)