logo

HAUSA

Dakarun Rasha sun kwace iko da masana’atar karafa ta Mariupol

2022-05-21 17:03:09 CMG Hausa

Ma’aikatar tsaron Rasha ta ce dakarun kasar sun kwace iko da masana’atar karafa ta Azovstal dake Mariupol na Ukraine.

Wata sanarwar da ma’aikatar ta fitar jiya, ta ce dakarun Rasha ne ke rike da ikon ginin karkashin kasa da mayakan Ukraine suka buya a baya.

Ta kara da cewa, rukuni na karshe na mayaka 531 sun mika wuya a jiya, inda ta ce duk tun daga ranar 16 ga wata, jimilar mayaka 2,439 da suka hada da ‘yan Nazi da sojojin Ukraine, sun ajiye makamansu.

A cewar sanarwar, ministan tsaron kasar Sergei Shoigu, ya bada rahoton kammaluwar aikin ga shugaba Vladimir Putin. (Fa’iza Mustapha)