logo

HAUSA

WHO ta kira taron gaggawa yayin da aka samu mutane sama da 100 da suka kamu da kyandar biri a Turai

2022-05-21 17:14:44 CMG Hausa

Bayan samun sama da mutane 100 da aka tabbatar ko ake zargin sun kamu da cutar Kyandar Biri a Turai a baya-bayan nan, hukumar lafiya ta duniya za ta gudanar da taron gaggawa domin tattaunawa game da barkewar cutar wadda aka fi samunta a yammaci da tsakiyar Afrika.

A wani abu da Jamus ta kira barkewa mafi girma a Turai, an tabbatar da samun wadanda suka kamu da cutar a akalla kasashe 5 da suka hada da Birtania da Spaniya da Portugal da Jamus da Italiya, har ma da Amurka da Canada da Australia.

Cutar wadda aka fara gano ta a tsakanin birrai dake yaduwa ta hanyar mu’amala, ba kasafai ake samunta a wajen nahiyar Afrika ba, don haka, batun ya zama abun damuwa.

Sai dai, masana kimiyya ba sa tsammanin barkewar cutar za ta zama annobar duniya kamar COVID-19, bisa la’akari da cewa, kwayar cutar ba ta da saukin yaduwa kamar ta COVID-19. (Fa’iza Mustapha)