logo

HAUSA

Wang Wenbin ya amsa tambayoyin manema labarai game da goyon-bayan da aka nunawa matsayin kasar Sin kan batun Taiwan a wajen taron WHO

2022-05-21 20:56:13 CMG Hausa

Za’a gudanar da babban taro karo na 75 na hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO daga ranar 22 zuwa 28 ga watan Mayun bana. Hukumomin kula da harkokin wajen yankin Taiwan sun nuna rashin jin dadi game da rashin samun gayyatar halartar taron.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Wang Wenbin ya ce, Sin kasa ce daya tak a duniya, kuma gwamnatin Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin halastacciyar gwamnati ce daya kadai dake wakiltar kasar. Taiwan kuma, wani bangare ne da ba za’a iya ware shi daga babban yankin kasar Sin ba. Ya ce ya kamata a daidaita batutuwan da suka shafi shigar yankin Taiwan kungiyoyin kasa da kasa, ciki har da WHO, bisa manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya.

Daga shekara ta 2009 zuwa ta 2016, duba da yadda dukkan gabobin biyu na mashigin tekun Taiwan suka girmama manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, kasar Sin ta yi shiri na musamman don halartar yankin Taiwan babban taron WHO. Amma tun bayan da jam’iyyar DPP ta kama mulkin yankin, ya zuwa yanzu, tana yunkurin balle yankin daga cikin kasar Sin, kuma ba ta amince da manufar kasancewar kasar Sin daya tilo a duniya ba, al’amarin da ya kawar da tushen siyasa na halartar yankin Taiwan babban taron WHO.

Gwamnatin kasar Sin tana matukar maida hankali kan zaman lafiya da rayuwar al’ummar Taiwan, kuma bisa tushen manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, gwamnatin kasa ta kan shiryawa Taiwan damammakin halartar harkokin kiwon lafiyar duniya. Wasu maganganun dake cewa, wai rashin halartar yankin Taiwan taron WHO, zai kawo cikas ga cika tsarin kandagarkin yaduwar annobar COVID-19 a duniya, karya ce zalla.

Irin wannan kudirin gwamnatin kasar Sin ya samu goyon-baya da fahimta sosai daga wajen kasa da kasa, inda kawo yanzu kasashe kusan 90, sun gabatar da sako zuwa ga hukumar WHO, don shaida matsayinsu na tsayawa kan manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, da adawa da halartar yankin Taiwan babban taron WHO. (Murtala Zhang)