logo

HAUSA

Babban darektan hukumar IAEA ya yi tsokaci kan shirin zubar da ruwan dagwalo zuwa teku

2022-05-21 16:26:56 CMG Hausa

Kafin kawo karshen ziyararsa ta yini uku a Japan, babban darektan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya Rafael Grossi, ya shirya taron manema labarai a birnin Tokyo da yammacin jiya Jumma’a, inda ya jaddada cewa, al’ummar Japan, da kasashe da yankuna makwabtanta, suna da hakkin bayyana damuwa kan shirin gwamnatin kasar na zuba ruwan dagwalo a cikin teku, kuma IAEA za ta ci gaba da tantance shirin.

Har wa yau, jama’ar Japan na ci gaba da nuna adawa kan wannan shirin. Ko a jiyan, kungiyoyin fararen-hula da dama sun yi gangami a gaban babbar kotun dake birnin Tokyo, inda suka goyi bayan mazauna gundumar Fukushima na dorawa kamfanin wutar lantarki na Tokyo laifin aukuwar hatsarin yoyon makamashin nukiliya. Kana masu gangamin sun ce ba su amince da shirin kamfanin wutar lantarki na Tokyo na zuba ruwan dagwalo a cikin teku ba. (Murtala Zhang)