logo

HAUSA

An cimma nasarori wajen taron ministocin harkokin wajen kasashen BRICS

2022-05-20 21:00:04 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a yau Jumma’a cewa, an cimma matsaya, da nasarori a wasu muhimman batutuwan da suka shafi tsaro da ci gaban duniya, a wajen taron ministocin harkokin wajen kasashen BRICS da aka yi ta kafar bidiyo a jiya Alhamis, matakin da ya share fage sosai a fannin siyasa, da gudanar da ganawar shugabannin kasashen BRICS karo na 14.

Jiya Alhamis, memban majalisar gudanawar kasar Sin, wanda kuma shi ne ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya jagoranci shawarwari ta kafar bidiyo, tsakanin ministocin harkokin waje na kasashen BRICS, da na kasashen dake da sabbin kasuwanni, da na kasashe masu tasowa. Ministocin harkokin waje, ko kuma wakilansu daga kasashen BRICS, da na Kazakhstan, da Saudiyya, da Argentina da sauransu, sun halarci shawarwarin.

Wang Wenbin ya jaddada cewa, wannan salon hadin-gwiwa da ake kira “BRICS+”, dandali ne da aka kafa ga kasashen dake da sabbin kasuwanni da kasashe masu tasowa. Kasar Sin na maraba da karin kasashe su shiga ciki, don kara shimfida tafarkin demokuradiyya a huldodin kasa da kasa, da raya tattalin arzikin duniya don amfanin kowa da kowa, da kuma tafiyar da harkokin mulkin duniya yadda ya kamata, a wani kokari na kirkiro makoma mai haske. (Murtala Zhang)