logo

HAUSA

Kasar Sin ta yi kira ga kasashen duniya da su kara hada hannu wajen daidaita kasuwar abinci ta duniya

2022-05-20 11:20:08 CMG Hausa

Jakadan kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya bukaci kasashen duniya su hada hannu wajen daidaita kasuwar abinci ta duniya, domin tabbatar da hanyoyi daban daban na samar da abinci da saukaka cinikayyar kayayyakin gona a duniya.

A cewar Zhang Jun, yayin da ake cikin zamani na dunkulewar duniya, duk wani cikas ga tsarin samar da kayayyaki zai yi tasiri ga sauran bangarori, yana mai cewa, neman amfana daga dogaro da tattalin arzikin kasashe suka yi da juna, haifar da wahalhalun da za a iya kaucewa kawai zai yi, tare da ta’azzara barazana a cikin gida.

Da yake tsokaci kan agajin gaggawa, jakadan na Sin ya ce bisa la’akari da yadda karancin abinci zai yi kamari, ya kamata kasashen duniya musamman manya, su kara samar da agajin abinci da taimakon da ake bukata na gaggawa, tare da kai dauki kan kari ga rukunoni masu rauni kamar mata da yara.

Zhang Jun ya kara da cewa, karfafa tsarin samar da abinci a duniya ta yadda zai iya jure barazana, na da matukar muhimmanci wajen karfafawa kasashe masu tasowa gwiwar tsayawa da kafarsu da kara raya ayyukan gona da karkara da gaggauta samun ci gaba a fannin kimiyya da fasahar aikin gona da inganta kayayyakin aikin gona da kuma fadada wadatar abinci. (Fa’iza Mustapha)