logo

HAUSA

Kasar Sin ta yi kira ga kasashen BRICS da su dauki matsaya guda yayin da duniya ke fuskantar kalubale

2022-05-20 11:33:34 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya ce yayin da ake fuskantar kalubale a duniya, akwai bukatar dangantakar kasashen BRICS ta dace da yanayin duniyar, kana su dauki matsaya guda da kara kwarin gwiwarsu tare da kokarin tunkarar sauye-sauyen duniya.

Wang Yi ya bayyana haka ne yayin da yake jagorantar taron ministocin harkokin wajen kasashen BRICS ta kafar bidiyo a jiya.

Ya ce taron ministocin harkokin wajen BRICS muhimmin dandali ne na hadin gwiwar tsaro da harkokin siyasa, yana mai cewa, ya kamata kasashen na BRICS su nemi tsaro na bai daya, da aiki tare domin samun ci gaba na bai daya. Kazalika akwai bukatar su yi kokarin samar da tsarin kare lafiyar bil adama da rajin tabbatar da shugabancin duniya bisa tuntubar juna da kuma bayar da gudunmuwa da samun moriya tare.

Wang Yi ya kuma jadadda cewa, akwai bukatar dukkan bangarori su kara zurfafa tuntuba da hadin gwiwa da aminci da juna, tare da zurfafa hadin gwiwar moriyar juna a fannoni daban-daban.

Ya kuma bayyana managartan ayyukan kasar Sin yayin da take rikon ragamar shugabancin karba-karba na kungiyar. Baya ga haka, kasar Sin ta yi alkawarin zurfafa hadin gwiwar kasashen kungiyar da inganta tasirinsu a harkokin duniya da kare maradun matsakaita da kananan kasashe masu tasowa. (Fa’iza Mustapha)