logo

HAUSA

Wang Wenbin: Fatanmu shi ne Amurka ta aiwatar da abubuwan da ta alkawarta

2022-05-20 20:49:51 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce kasar sa na fatan Amurka za ta inganta kawancen ta da kasashen dake yankin Asiya da tekun Pacifik, za ta kuma kara azama wajen ingiza zaman lafiya da ci gaba, maimakon rura wutar rikici, da tada zaune tsaye a yankin. Wang ya bayyana hakan ne yayin taron manema labarai na Juma’ar nan a birnin Beijing

A yau Juma’a ne shugaban Amurka Joe Biden ya isa Koriya ta Kudu, inda zai gana a karon farko da sabon shugaban kasar Yoon Suk-yeol. Kuma tun a ranar Laraba ne, mashawarcin shugaban na Amurka ta fuskar tsaron kasa Jake Sullivan, ya bayyana cewa, ziyarar da shugaba Biden din zai gudanar a nahiyar Asiya, ba ta da nasaba da yin fito-na-fito da kasar Sin.

Game da hakan, Wang ya ce abun fatan dai shi ne Amurka ta aiwatar da abubuwan da ta alkawarta, ta kuma yi aiki tare da sauran kasashen yankin tekun Indiya da Pacific da Asiya, don yayata dunkulewa da hadin gwiwa, maimakon kitsa matakan rarrabuwar kawuna da fito na fito.

Game da batun tsarin nan na ingiza tattalin arzikin yankin, wadda Amurka ta tsara kaddamarwa yayin ziyarar ta Mr. Biden, Wang ya ce Sin na da ra’ayin cewa, ya kamata duk wani tsari na shiyya ya dace da zamanin da ake ciki, ta yadda hakan zai haifar da yanayin zaman lafiya da ci gaba, kana ya kamata tsarin ya ingiza amincewa da juna, da hadin gwiwa tsakanin kasashen shiyyar, ya kuma kunshi kowa da kowa ba tare da wariya ba. Kaza lika bai dace a yi amfani da shi wajen muzgunawa wani bangare ba. (Saminu)