logo

HAUSA

Kwamitin sulhun MDD ya kira taron magance matsalar karancin abinci

2022-05-20 10:51:49 CMG Hausa

Jiya ne, kwamitin sulhu na MDD ya kira wani taro, don magance matsalar karancin abinci, inda ya yi kira ga kasashen duniya, da su karfafa hadin gwiwa don warware wannan matsala.

Babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya shaida wa kwamitin sulhun a yayin wata muhawara kan rikici da samar da abinci, wanda sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken ya jagoranta cewa, a duk lokacin da yaki ya barke, jama’a ne ke shiga yunwa.

Babban jami'in na MDD ya ce, kusan kashi 60 cikin 100 na mutanen da ba su da abinci a duniya, suna zaune ne a yankunan da rikici ya shafa. Yana mai cewa, babu wata kasa da za ta tsira.

A bara, yawancin mutane miliyan 140 da ke fama da matsananciyar yunwa a duniya, suna zaune ne a kasashe 10 kacal: wato Afghanistan, da Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, da Habasha, da Haiti, da Najeriya. Sauran kasashen su ne Pakistan, da Sudan ta Kudu, da Sudan, da Syria da Yemen, kuma takwas daga cikinsu, suna cikin ajandar majalisar.

Duk da jin dadin sanarwar cewa, asusun ba da agajin gaggawa na majalisar zai samar da dalar Amurka miliyan 30, don biyan bukatun samar da abinci a Nijar, da Mali, da Chadi, da Burkina Faso, babban jami'in MDDr ya bayyana cikin bakin ciki cewa, " kamar digon ruwa ne a cikin teku." (Ibrahim)