logo

HAUSA

Dakarun Najeriya sun kashe mayakan kungiyar yan ta’adda 43

2022-05-20 10:22:04 CMG Hausa

Sojojin Najeriya sun kashe a kalla mayakan kungiyar masu tsattsauran ra’ayi 43 a shiyyar arewa maso gabashin kasar a cikin makonni ukun da suka gabata, a ayyukan sintirin yaki da ’yan ta’adda da suka kaddamar a shiyyar, kamar yadda rundunar sojojin kasar ta bayyana.

Bernard Onyeuko, kakakin rundunar sojojin Najeriya, ya bayyanawa manema labarai a Abuja, babban birnin kasar cewa, sojojin sun kuma yi nasarar kama wasu daga cikin mayakan 20, kana sun kubutar da mutane 63 wadanda ’yan ta’addan suka yi garkuwa da su a wurare daban-daban a shiyyar arewa maso gabashin kasar, tsakanin ranar 28 ga watan Afrilu zuwa 19 ga watan Mayu.

Ya ce, sojojin sun samu nasarori masu yawan gaske a lokacin kaddamar da hare-haren, daga ciki, sun yi nasarar kashe wani babban jagoran kungiyar Boko Haram wanda aka fi sani da Malam Shehu, da sauran mukarrabansa a lokacin da sojojin ke gudanar da ayyukan murkushe ’yan ta’addan, a sansanoninsu dake garuruwan Jaje, Mango Ali, Dissa, Balangaje, a jahar Borno dake shiyyar arewa maso gabashin Najeriya. (Ahmad)