logo

HAUSA

Shugabannin kasashen Sin da Timor-Leste sun tuya juna murnar cika shekaru 20 da kulla huldar diflomasiyya

2022-05-20 14:55:29 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, da takwararna na kasar Timor-Leste, Jose Ramos-Horta, a yau Juma’a sun aike da sakonnin taya juna murnar cika shekaru 20 da farfado da ’yancin kan kasar Timor-Leste da kuma kulla huldar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu.

Tun bayan kulla huldar diflomasiyyar shekaru 20 da suka gabata, bangarorin biyu suna kara zurfafa huldar siyasa, da amincewar juna, da samun gagarumar nasara ta hakikanin hadin gwiwa, da kuma samun kyautatuwar hulda tsakanin mutum da mutum, da musayar al’adu, lamarin da ke nuna samun muhimmin ci gaban huldar dake tsakanin kasashen biyu.

Da yake jaddada irin muhimmancin da yake bayarwa game da cigaban huldar dake tsakanin Sin da Timor-Leste, shugaban kasar Sin ya ce, yana aiki tare da Ramos-Horta, domin tabbatar da kara kyautata huldar dake tsakaninsu bangarorin biyu, da kyautata abota, da amincewar juna, don amfanawa bangorin biyu zuwa wani sabon mataki, domin hidimtawa kasashen biyu da kuma al’ummunsu. (Ahmad)