logo

HAUSA

Ya kamata Amurka ta dakatar da amfani da babban taron WHO don rura wutar rikici kan batun Taiwan

2022-05-19 20:51:30 CMG Hausa

A kwanan nan ne kasar Amurka ta yi kira ga hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO, da ta gayyaci yankin Taiwan don zama ‘yar kallo a hukumar. Game da wannan batu, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Zhao Lijian ya ce, kasarsa na adawa da irin wannan kira na Amurka, inda ta nemi Amurka ta dakatar da rura wutar rikici kan batun da ya shafi yankin Taiwan, bisa hujjar babban taron WHO.

Wasu rahotannin sun ce, sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken ya fitar da wata sanarwa a jiya Laraba, inda ya shawarci hukumar WHO da ta gayyaci Taiwan a matsayin ‘yar kallo, yayin babban taron WHO karo na 75 da za’a yi a wannan wata.

Zhao ya ce, kasar Sin daya ce tak a duniya, kuma Taiwan wani sashi ne da ba za’a iya balle shi daga yankin kasar ba. Duk wani batun da ya shafi halartar yankin Taiwan a ayyukan kungiyoyin kasa da kasa, ciki har da WHO, ya zama dole a daidaita shi bisa babbar manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya. (Murtala Zhang)