logo

HAUSA

Manyan jami'an diflomasiyya na kasashen Sin da Amurka sun yi tattaunawa ta wayar tarho

2022-05-19 10:19:05 CMG Hausa

Mamban ofishin siyasa na kwamitin koli na JKS Yang Jiechi, jiya Laraba ya tattauna ta wayar tarho da mai ba da shawara kan harkokin tsaron kasar Amurka, Jake Sullivan, bisa bukatar da ya gabatar.

Yang, wanda shi ne daraktan ofishin kula da harkokin waje na kwamitin tsakiya na JKS, ya ce, kamata ya yi kasashen biyu su aiwatar da muhimmin ra'ayi da shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na Amurka Joe Biden suka cimma kan dangantakar kasashen biyu.

Yang ya kara da cewa, kamata ya yi Amurka ta martaba kalamai da ayyukanta, ta cika alkawuran da ta dauka ta hanyar aiwatar da sahihan manufofi da ayyuka, da hada kai da kasar Sin, ta kuma daidaita bambance-bambancen dake tsakanin bangarorin biyu yadda ya kamata, da kara yin wasu abubuwa masu ma'ana, da za su maido da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu bisa turbar da ta dace da samun ci gaba mai inganci.

Wang ya ce, batun da ya shafi Taiwan, batu ne mai mahimmanci kuma babbar tambaya ce game da alakar dake tsakanin Sin da Amurka. Yana mai jaddada cewa, bangaren Amurka ya sha bayyanawa karara a lokuta da dama cewa, yana martaba manufar Sin daya tak a duniya, kuma baya goyon bayan 'yancin kai na Taiwan. Amma duk da haka, abubuwa da Amurka ta yi a baya-bayan nan game da batun Taiwan, sun yi hannun riga da abubuwan da take fada. Yana mai cewa, idan har bangaren Amurka ya ci gaba da wasa da "batun yankin Taiwan" tare da ci gaba da bin hanyar da ba ta dace ba, ko shakka babu zai jefa lamarin cikin mummunan hadari. (Ibrahim)