logo

HAUSA

Xi ya amsa wasikar da masana matasa da suka dawo daga ketare suka rubuta masa

2022-05-19 14:42:16 CMG Hausa

Jiya Laraba shugaban kasar Sin Xi Jinping ya amsa wasikar da masana matasa dake aiki a jami’ar Nanjing ta lardin Jiangsu da suka kammala karatu a kasashen ketare suka rubuta masa, inda ya yi musu kyakkyawan fata.

Cikin wasikar, Xi ya yi tsokaci cewa, yana farin ciki matuka da yadda suke daukar tsoffin masana kimiyya kamar su Li Siguang da Cheng Kaijia a matsayin abin koyi, kuma sun dawo gida bayan da suka kammala karatu a kasashen ketare, haka kuma suna kokarin gudanar da aikin ba da ilmin kimiyya a jami’a, domin bautawa al’ummun kasar. Yanzu haka  ana murnar cika shekaru 120 da kafa jami’ar Nanjing, Xi yana fatan alheri ga dukkanin malamai da daliban jami’ar.

Kwanan baya wakilan masana matasa 120 dake aiki a jami’ar Nanjing bayan da suka kammala karatu a ketare, sun aika wata wasika ga shugaba Xi, inda suka bayyana ra’ayoyinsu kan aikin ba da ilmi da kirkire-kirkire wajen nazarin kimiyya, tare kuma da nuna aniyarsu ta yada al’adun gargajiyar al’ummun Sinawa da sauke sauyin dake bisa wuyansu na raya kasar ta Sin. (Jamila)