logo

HAUSA

An gabatar da shawarar Beijing na taron kolin raya zuba jari da cinikayyar duniya

2022-05-19 11:46:01 CMG Hausa

 

Jiya Laraba ne, aka kira taron cika shekaru 70 da kafuwar hukumar yayata hada-hadar cinikayyar kasa da kasa ta kasar Sin, da taron kolin kasa da kasa na ingiza harkokin cinikayya da zuba jari da ya gudana ta kafar bidiyo a birnin Beijing, inda wannan hukumar kasar Sin da wakilan hukumomin yayata hada-hadar cinikayyar kasa da kasa da sassan masana’antu na kasashe da yankuna 59 suka gabatar da shawarar Beijing game da taron kolin sa kaimi ga zuba jari da cinikayyar duniya. Shawarar ta yi fatan yin hadin gwiwa don tinkarar kalubalen cutar COVID-19, da inganta daidaito da farfado da tattalin arzikin duniya da masana’antu, da hada kai wajen warware gibin bunkasuwa, ingiza aikin kirkire-kirkire, da sa kaimi ga samun dauwamammen ci gaba ta hanyar kiyaye muhallin halittu.

Muhimman kusoshin siyasa na kasashe daban daban da na kungiyoyin duniya masu halartar taron, sun taya hukumar cika shekaru 70 da kafuwa. Sun kuma yi imanin cewa, hukumar ta bayar da gudummarwar a zo a gani ga farfadowar tattalin arzikin duniya, tare da fatan inganta hadin kai da Sin wajen samun ci gaba mai dorewa bayan annobar cutar.

Ngozi Okonjo-Iweala, babbar daraktar kungiyar WTO ta bayyana cewa, ko da yaushe, hukumar yayata hada-hadar cinikayyar kasa da kasa ta kasar Sin na dukufa wajen kara azama ga cinikayaya, zuba jari da hadin kan tattalin arziki tsakanin Sin da kasashe daban daban. Yayin da ake tinkarar matsalolin yaduwar cutar COVID-19, da rikice-rikice, da karancin hatsi, da lalacewar muhallin halittu a halin yanzu, hadin kai a tsakanin kasa da kasa yana da muhimmanci matuka fiye da ko wane lokaci. (Kande Gao)