logo

HAUSA

Sin ta bukaci Amurka ta dakatar da fakewa da batun Tibet wajen tsoma baki a harkokin gidanta

2022-05-19 20:17:02 CMG Hausa

A yau Alhamis ne kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya jaddada kira ga kasar Amurka, da ta dakatar da fakewa da batutuwan da suka shafi jihar Tibet, wajen tsoma baki cikin harkokin gidan ta.

Zhao Lijian ya yi wannan kira ne, a matsayin martani ga tambayar da aka yi masa dangane da yadda jami’ ar tsare tsare ta musamman mai kula da harkokin Tibet Uzra Zeya, wadda kuma ita ce mataimakiyar sakataren harkokin wajen kasar Amurka a jiya Laraba ta zanta da jagoran bangaren dake kiran kan su da "Gwamnatin Tibet mai gudun hijira" a kasar India.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Sin, ya jaddada cewa, wadannan mutane dake kiran kan su da "Gwamnatin Tibet mai gudun hijira" ‘yan a ware ne na siyasa, wadanda ke gudanar da haramtattun ayyuka da suka sabawa kundin tsarin mulkin kasar Sin, da ma dokokin kasar, kuma kungiya ce da ba ta da goyon bayan ko da kasa daya tak a duniya.

Zhao ya kara da cewa, Dalai Lama na 14, ba wai cikakken jagoran addini ba ne, maimakon haka dan gudun hijirar siyasa ne da ya jima yana shugabantar ayyukan ‘yan aware, tare da yunkurin balle Tibet daga kasar Sin.(Saminu)