logo

HAUSA

Sama da kamfanoni 240 wadanda suke kan gaba a duniya sun rattaba hannu kan kwangiloli a bikin baje kolin CIIE karo na biyar

2022-05-19 10:35:52 CMG Hausa

Ofishin CIIE ya bayyana a jiya Laraba cewa, shirye-shiryen bikin baje kolin kasa da kasa na kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin karo na biyar, na ci gaba da tafiya yadda ya kamata, inda kamfanoni sama da 240 daga cikin manyan kamfanoni 500 na duniya sun rattaba hannu kan kwangilolin halartar bikin baje kolin CIIE karo na biyar, sannan ya zuwa yanzu, fadin rumfunan da kamfanoni wadanda za su halarci bikin suka amince da yin haya ya kai kashi 70 cikin 100 na dukkan rumfunan bikin baje kolin da za a gudanar. Galibin masu baje kolin na kasashen waje, sun bayyana fatansu na ci gaba da amfana da kasuwannin kasar Sin, da kara samun bunkasuwa.

Shugaban sashen rukunin kamfanin harhada magunguna na Pfizer Biopharmaceutical dake kasar Sin Jean-Christophe Pointeau, ya yi imanin cewa, manufar kasar Sin ta bude kofa ga waje, tana da matukar muhimmanci ga yanayin da duniya ta tsinci kanta sanadiyar illar da cutar COVID-19 ta haifar, kuma yadda Sin take ci gaba da bude kofa ga kasashen waje, hakan na kara karfafa gwiwar kamfanonin na shiga cikin harkokin raya tattalin arzikin kasar Sin. (Ibrahim)