logo

HAUSA

Xi Jinping ya gabatar da jawabi ga taron ministocin wajen kasashe mambobin kungiyar BRICS

2022-05-19 21:28:47 CMG Hausa

A yau Alhamis ne shugaban kasar Sin Xi jinping, ya gabatar da jawabi a yayin bude taron ministocin wajen kasashe mambobin kungiyar BRICS ta kafar bidiyo.

Cikin jawabin na sa, Xi Jinping ya ce a halin yanzu, dalilan dake haifar da rashin kwanciyar hankali, da rashin tabbas, da rashin tsaro a harkokin kasa da kasa na kara bayyana. Amma duk da haka, jigon wannan zamanin da muke ciki na zaman lafiya, da neman ci gaba bai canza ba, kaza lika burin al’ummun duniya na samun kyakkyawar rayuwa bai sauya ba, haka kuma, fatan sassan kasa da kasa na aiki tare kafada da kafada, da hadin gwiwa domin cimma moriyar juna shi ma bai canza ba.

Bugu da kari, Xi ya jaddada cewa, tarihi da ainihin abubuwan da ke faruwa na nuna cewa, yunkurin wata kasa guda na samar da tsaron kashin kan ta, yayin da wata ke fuskantar barazana, ba abun da zai haifar sai rudani. Don haka a cewar sa “Domin bunkasa zaman lafiya da tsaron duniya, a baya bayan nan, na gabatar da shawarar samar da tsaro ta kasa da kasa”. Shugaban na Sin ya ce, ya kamata kasashe mambobin kungiyar BRICS su karfafa amincewa da juna ta fuskar siyasa, da hadin gwiwar tsaro, su kuma ci gaba da tattaunawa, da tsara ayyuka tare, don gudanar da batutuwan kasa da kasa da na shiyyoyi yadda ya kamata. Kaza lika ya dace su marawa juna baya, wajen kare muhimman moriyar kawunan su, su martaba ikon mulkin kai, da tsaro da moriyar ci gaban juna. Kaza lika su nuna rashin amincewa da danniya da siyasar nuna fin karfi, su kuma yi adawa da cacar baka, da daukar matakan yin fito na fito da juna, tare da gina al’ummar duniya mai cikakken tsaro.

Shugaba Xi ya jaddada cewa, ci gaba buri ne na dukkanin kasashe masu karsashin kasuwanni da kasashe masu tasowa. Don haka ya kamata kasashen nan 5 su tattauna, tare da yin musaya tare da karin kasashe masu karsashin kasuwanni da kasashe masu tasowa, a fannin inganta fahimtar juna da amincewa juna, su karfafa hadin gwiwa, da fadada moriyar hadin gwiwa, su ingiza matakan ci gaba, tare da ba da karin gudunmawar cimma nasarar kyakkyawan fata, na gina al’umma mai makomar bai daya ga dukkanin bil adama. (Saminu)