logo

HAUSA

Kasar Sin za ta kara samar da damammaki ga kamfanonin ketare don su zuba jari a kasar

2022-05-18 20:42:09 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a yau Laraba cewa, idan an yi hangen nesa, za a ga yadda tattalin arzikin kasar zai samu habaka mai dorewa, da kuma makoma mai haske. Ya ce kasar Sin za ta ci gaba da zurfafa yin kwaskwarima a gida, da fadada bude kofa ga kasashen waje, da kyautata yanayin kasuwanci dake bin doka da oda irin na duniya, domin kara samar da damammaki ga kamfanonin kasashe daban-daban, ciki har da na Amurka, wajen zuba jari da gudanar da harkokin kasuwanci.

Rahotannin sun ce, kungiyar kamfanonin Amurka dake kasar Sin, ta bullo da wata takardar bayani game da kamfanonin Amurka dake kasar Sin a shekara ta 2022, inda ta bayyana cewa, kungiyar na adawa da rarrabuwar kawuna tsakanin kasashen biyu, tana kuma goyon-bayan fadada soke harajin kwastam da aka bugawa hajojin Sin, kana tana adawa da siyasantar da batun COVID-19, gami da manufofin dakile yaduwarta. Jami’an kungiyar sun ce, kasar Sin tana da babban burin samar da ci gaba, da dimbin damammakin kasuwanni, gami da yanayin kasuwanci mai kyakkyawar makoma, al’amarin dake janyo hankalin kamfanonin Amurka sosai. (Murtala Zhang)