logo

HAUSA

Lavrov: hakika Ukraine ta janye daga shawarwarin da ake yi tsakaninta da Rasha

2022-05-18 12:08:46 CMG HAUSA

 

Kamfanin dillancin labaru na kasar Rasha, ya ruwaito ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov a jiya yana cewa, hakika kasar Ukranei ta janye daga Shirin tattaunawa tsakaninta da Rasha. A wannan rana kuma, Mykhailo Podolyak, mashawarcin ofishin shugaban Ukraine ya nuna cewa, an dakatar da shirin shawarwarin tsakanin Ukraine da Rasha.

A cewar Lavrov, kasashen yammacin duniya na fatan a jinkirta shawarwarin, a yunkurin haddasa hasara da ma durkushewar bangaren Rasha. Kasashen yammacin duniya sun ayyana Ukraine a matsayin sadaukarwa a yakin da suke yi da kasar Rasha. (Tasallah Yuan)