logo

HAUSA

Shugaba Xi ya jaddada aniyar kasar sa ta bude kofa mai nagarta

2022-05-18 21:55:25 CMG Hausa

A yau Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada aniyar kasar sa ta bude kofa mai nagarta, yana mai cewa Sin za ta ci gaba da bude kofa ga duniya baki daya, ba tare da sauya matsaya ba.

Xi ya yi wannan tsokaci ne, yayin da yake jawabi ga taron cika shekaru 70 da kafuwar hukumar yayata hada hadar cinikayyar kasa da kasa, da taron kolin kasa da kasa na ingiza harkokin cinikayya da zuba jari, da ya gudana ta kafar bidiyo. (Saminu)