logo

HAUSA

Sweden da Finland za su gabatar da takardar bukatarsu ta shiga NATO Larabar nan

2022-05-18 09:51:35 CMG Hausa

Firaministar kasar Sweden Magdalena Andersson ta sanar a jiya cewa, kasashen Sweden da Finland, za su gabatar da takardarsu ta neman zama mamban kungiyar tsaro ta NATO cikin hadin gwiwa a yau Laraba.

Magdalena ta bayyana a yayin wani taron manema labarai da shugaban kasar Finland Sauli Niinisto dake ziyara a kasar ya halarta cewa, mambobin kungiyar tsaro ta NATO za su karfafa tsaro a kasar Sweden da ma yankin tekun Baltic.

Ta kara da cewa, gabatar da aikace-aikacen hadin gwiwa tare da Finland, yana nufin za mu iya ba da gudummawar tsaro a arewacin Turai.

Sai dai shugaban Rasha Vladimir Putin ya fada a ranar Litinin cewa, Moscow za ta mayar da martani, idan har NATO za ta tura kayayyakin aikin soji a yankunan Finland ko Sweden.

A cewar gwamnatin Sweden, Niinisto yana ziyara a kasar Sweden ne, tun daga jiya Talata zuwa yau Laraba. Gobe Alhamis ne kuma, aka shirya Andersson da Niinisto za su gana da shugaban Amurka Joe Biden a Washington. (Ibrahim)