logo

HAUSA

Johns Hopkins: Adadin Amurkawan da COVID-19 ta kashe sun zarce miliyan guda

2022-05-18 10:14:11 CMG Hausa

Kasar Amurka ta kafa tarihi mai muni yayin da adadin Amurkawan da annobar COVID-19 ta kashe ya zarce miliyan 1 ya zuwa ranar Talata, kamar yadda alkaluman jami’ar Johns Hopkins suka bayyana.

Yayin da kasar ke da adadin mutane miliyan 82.6 da suka kamu da cutar, yawan mutanen da suka mutu a fadin kasar ta Amurka ya kai 1,000,004 ya zuwa karfe 12:20, agogon gabashin yankin Amurka, wato daidai da karfe 16:20 agogon GMT na ranar Talatar, kamar yadda alkaluman suka nuna.

Amurka ta kasance a matsayin kasar ta annobar ta fi muni a duniya, yayin take da kaso mafi yawa na mutanen da suka kamu, da kuma adadin wadanda cutar ta hallaka a duk duniya, dukka adadi kamuwar da na wadanda da suka mutu a kasar ya kusan kaiwa kashi 16 bisa 100 na jimillar adadin na duniya baki daya. (Ahmad)