logo

HAUSA

Mahakurci Mawadaci

2022-05-18 17:54:17 CMG Hausa

A dai-dai gabar da annobar COVID-19 ke ci gaba da addabar sassan duniya, yankin yammacin Afirka ya kama hanyar fara samar da alluran riga kafin cututtuka daban-daban. Babban darektan hukumar lafiya ta yammacin Afrika (WAHO) Stanley Okolo, shi ne ya sanar da wannan albashir, yayin wani taron manema labarai da aka shirya, bayan kammala taro karo na 23 na ministocin lafiya na kasashe mambobin kungiyar ECOWAS.

Daga cikin alluran riga kafin da ake fatan yankin zai fara samarwa, har da na COVID-19 da cutar shawara da cizon kare da na maciji, abin da masu sharhi ke cewa, zai sanya yankin zama mai dogaro da kansa wajen samar da rigakafi da ma wadatarsu. Matakin da hakika zai share hawayen  nahiyar Afirka baki daya a fannin riga kafi da ma sauran magunguna

Stanley ya ce, a kokarin ganin wannan mafarki ya tabbata, har sun tuntubi kamfanoni 5 da nazari ya nuna cewa, yanzu haka sun kama hanyar samar da rigakafin a yankin. Kuma biyu  daga cikinsu kamfanoni ne na kasar Ghana, 2 kuma na Najeriya sai kuma 1 daga kasar Senegal.

Bayanai na nuna cewa, daga matsakaici zuwa dogon zango, yankin zai iya samar da nau’o’in alluran riga kafi 22 da zarar an karfafa masana’antarsa na harhada magunguna.

Bugu da kari, hukumar WAHO, ta hada kai da hukumar raya masana’antu ta MDD, domin samar da dabarun da za su tabbatar da cewa, kamfanonin harhada magungunan na aiki yadda ya dace, a matsayin wani mataki na tabbatar da cewa, ingancin kayayyakin da za su samar, ya kai mazanin da ake bukata.

A cewar masana, idan har wannan shiri na samar da alluran riga kafi a nahiyar ya tabbata, ba ya ga kawancen Sin da Afirka na samar da riga kafi a wasu daga cikin kasashen nahiyar ci gaba ba ne, ba kawai ga kasashen dake yankin ba, har ma ga nahiyar Afirka baki daya. Matakin da zai dakile kokarin da wasu kasashen yamma ke yi na mallake irin wadannan riga kafi, a lokacin da kasashen duniya, musamman kasashe masu tasowa ke matukar bukatar riga kafin, don kawo karshen wannan annoba. Mai hakuri aka ce ya kan dafa dutse, har ma ya sha romonsa. (Ibrahim Yaya)