logo

HAUSA

Sin na adawa da kudin-goro da Amurka ke yi game da batun tsaron kasa da matakan ta na muzgunawa kamfanonin wasu kasashe

2022-05-17 20:24:04 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a yayin taron manema labarai na yau Talata cewa, matakan zahiri da Amurka ke dauka, sun sabawa ka’idojin kasuwancin kasa da kasa, da sauran dokokin cinikayyar kasa da kasa, suna kuma gurgunta tsarin samar da hajojin da kasashen duniya ke sarrafawa.

Wang ya yi tsokacin ne a matsayin martani, game da wasu rahotanni dake cewa, Amurka na shirin kara hukunta kamfanonin da ta kira masu “keta ka’idojin fitar da hajoji zuwa ketare”.  (Saminu)