logo

HAUSA

Jirgi mai saukar ungulu kirar AC313A na kasar Sin ya yi tashi a karon farko

2022-05-17 13:50:33 CMG Hausa

 

Kamfanin jiragen sama na kasar Sin AVIC, ya ce babban jirgi mai saukar ungulu samfurin AC313A da kasar ta kera da kanta, ya samu nasarar tashi a karon farko a yau Talata.

Babban jirgi mai dakon kaya tonne 13, ya yi tashinsa na farko ne a filin jirgin saman Jingdezhen na lardin Jiangxi dake gabashin kasar Sin, wanda wani muhimmin mataki ne na inganta tsarin aikin ceto ta sama na kasar. Yanzu aikin kera jirgin AC313A zai shiga matakin gwaji .

Ana sa ran jirgin zai samu shaidar aiki yayin shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo 14 tsakanin shekarar 2021 zuwa 2025, daga nan kuma sai ya shiga kasuwa domin hidimtawa kwastomomi.

AC313A muhimmin samfurin jirgin sama ne da aka kera musamman domin biyan bukatun kasar na ayyukan ceto ta sama. Ana sa ran zai taimaka wajen karfafa karfi da tsarin ayyukan ceto ta sama na kasar Sin. (Fa’iza Mustapha)