logo

HAUSA

Wakilin Sin ya yi kira ga kasa da kasa su aiwatar da shirin raya kasashen duniya

2022-05-17 10:52:44 CMG Hausa

A jiya ne, wakilin Sin ya yi jawabi a gun taro na 23 na rukunin aiki mai kula da ’yancin samun bunkasuwa na gwmnatocin kasa da kasa na majalisar kare hakkin dan Adam ta MDD, inda ya jaddada muhimmiyar rawar da bunkasuwa ke takawa, wajen kare hakkin dan Adam, kana ya yi kira ga kasa da kasa, da su dora muhimmanci kan batun samun bunkasuwa, da aiwatar da shirin raya kasashen duniya.

Wakilin Sin ya bayyana cewa, cutar COVID-19 ta kawo babbar illa ga bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al’umma da kuma zaman rayuwar jama’ar kasa da kasa, musamman kasashe masu tasowa, hakan ya kara tsananta yanayin rashin adalci a duniya. Yayin da ake kokarin samun farfadowa bayan abkuwar cutar, al’ummomin kasashen duniya, suna kula da yadda aka samu bunkasuwa, kana suna aiwatar da ajandar samun bunkasuwa mai dorewa nan da shekarar 2030.

Wakilin Sin ya jaddada cewa, ya kamata kasa da kasa su ba da gudummawa a fannin kare hakkin dan Adam, da kiyaye ra’ayin samun bunkasuwa bisa tushen jama’a, da sa kaimi ga samun bunkasuwa tare, da daidaita matsalolin rashin daidaito da adalci a tsakanin kasa da kasa, ko a tsakanin wurare daban daban na kasa, da kuma kiyaye ra’ayin bangarori daban daban, da nuna goyon baya ga MDD wajen taka rawa kan hada kan kasa da kasa wajen aiwatar da ajandar samun bunkasuwa mai dorewa nan da shekarar 2030. (Zainab)