logo

HAUSA

Daga matsayin RMB a tsarin musayar kudi na SDR da IMF ta yi zai taimakawa RMB kara jawo hankalin duniya

2022-05-17 20:35:32 CMG Hausa

Asusun ba da lamuni na duniya wato IMF, ya sanar da karin darajar kudin kasar Sin na RMB, a cikin tsarin musayar kudaden ketare (SDR). Game da wannan batu, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Wang Wenbin ya bayyana cewa, wannan ita ce babbar amincewar da kasa da kasa suka nunawa kasar Sin, game da nasarorin da ta samu, a fannin aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, da kuma raya tattalin arziki da zaman rayuwar al’umma. Kana, hakan zai kara taimakawa wajen daga matsayin kudin Sin RMB bisa matsayin kudin ajiyar kasa da kasa, da taimakawa kudin kara jawo hankalin kasa da kasa.

Rahotannin sun ce, bayan kammala nazari na tsawon shekaru, IMF ta daga darajar RMB na kasar Sin, inda ta karu daga kashi 10.92 zuwa kashi 12.28 cikin 100. Wannan shi ne nazari na farko da aka yiwa tsarin na SDR , tun lokacin da RMB ya zama kudi na biyar a hukumance, a cikin tsarin musayar kudaden na SDR tun daga shekarar 2016. (Murtala Zhang)