logo

HAUSA

Wang Yi ya gana da sabon takwaran aikinsa na Koriya ta Kudu ta kafar bidiyo

2022-05-17 10:59:42 CMG Hausa

A jiya ne, memban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya gana da sabon takwaran aikinsa na kasar Koriya ta Kudu Park Jin ta kafar bidiyo, Yayin ganawar Wang Yi ya yi fatan Sin da Koriya ta Kudu za su bi hanyar da ta dace da yin kokari tare wajen raya dangantakarsu zuwa wani sabon matsayi nan da shekaru 30 masu zuwa.

Wang Yi ya bada shawarwari guda hudu, kan yadda za a raya dangantakar dake tsakanin Sin da Koriya ta Kudu a nan gaba. Na farko, ya kamata a kara yin mu’amala da yin imani da juna. Bisa jagorancin shugabannin kasashen biyu, sassan biyu sun kiyaye yin mu’amala da juna kan harkokin diplomasiyya da siyasa. Na biyu, ya kamata a kara yin hadin gwiwa da samun moriyar juna, don yin kokari tare wajen samun farfadowa. Na uku, a kara yin mu’amala kan al’adu a tsakanin kasashen biyu, da sada zumunta a tsakanin jama’arsu. Na hudu kuwa, a kara hadin gwiwa a tsakanin kasa da kasa don tabbatar da zaman lafiya a yankin.

A nasa bangare, minista Park Jin ya bayyana cewa, Koriya ta Kudu tana dore muhimmanci sosai kan raya dangantakar dake tsakaninta da Sin, tana kuma son girmama juna da yin hadin gwiwa don raya dangantakarsu yadda ya kamata. Kasar Koriya ta Kudu ta tsaya tsayin daka kan manufar Sin daya tak a duniya, ta kuma nuna yabo da ganin kasar Sin ta ci gaba da taka muhimmiyar rawa kan batun zirin Koriya. (Zainab)