logo

HAUSA

An cimma nasarar kawar da kwayoyin cutar COVID-19 baki daya a kananan hukumomi 16 na birnin Shanghai

2022-05-17 14:20:48 CMG Hausa

A yayin taron ganawa da manema labarai game da aikin kandagarkin annobar COVID-19 da aka shirya yau Talata da safe, an bayyana cewa, a halin yanzu, an cimma nasarar kawar da kwayoyin cutar COVID-19 baki daya a yankunan kananan hukumomi 16 dake birnin Shanghai na kasar Sin.

A jiya Litinin 16 ga wata, an tabbatar da sabbin mutane 77 da suka kamu da cutar, sannan wasu mutane 746 da suka kamu da cutar, amma ba tare da nuna alamun cutar ba a birnin Shanghai. Kuma, dukkansu suna zaune ne a cikin yankunan da aka kilace.

Bugu da kari, bisa nazarin da masana suka yi, za a dawo da harkokin yau da kullum a duk fadin birnin yadda ya kamata bisa matakai guda uku. Kuma, bisa shirin da aka tsara, daga ranar 1 ga watan Yuni zuwa tsakiyar watan Yuni, za a ci gaba da aiwatar da tsaurarrun matakan kandagarkin cutar bisa ka’idar rigakafin yaduwar cutar, da tafiyar da harkokin kasuwanci da aikin kandagarkin annoba yadda ya kamata. (Maryam)