logo

HAUSA

Kasuwannin Shanghai suna dawowa bakin aiki bisa matakai daban daban tun daga yau

2022-05-16 09:51:08 CMG Hausa

Mataimakin magajin garin birnin Shanghai Chen Tong, ya bayyana yayin taron ganawa da manema labarai game da aikin kandagarkin annobar COVID-19 da aka shirya jiya Lahadi da safe cewa, birnin Shanghai yana  kokari matuka, domin samar da isassun kayayyakin bukatun yau da kullum ga mazauna birnin, haka kuma ya zuwa yanzu, kasuwannin yanar gizo da suka dawo bakin aiki, sun karu zuwa 10625, inda kayayyakin da ake jigila zuwa ga masu sayayya, sun kai miliyan 5 a ko wace rana, kuma za a ci gaba da aiwatar da tsaurarrun matakan kandagarkin cutar bisa ka’idar “bude kasuwa bisa shirin da aka tsara, da takaita cudanya tsakanin mazauna birnin, da tafiyar da harkokin kasuwanci da aikin kandagarkin annoba yadda ya kamata”. Tun daga yau wato Litinin 16 ga wata, kasuwannin birnin Shanghai sun fara dawowa bakin aiki bisa matakai daban daban. (Jamila)