logo

HAUSA

Mutanen kasa da kasa sun tattauna hadin gwiwar “ziri daya da hanya daya”

2022-05-16 14:04:45 CMG Hausa

A ranar 14 ga watan Mayu, tagwayen hanyar mota dake birnin Nairobi, ita ce tagwayen hanyar irinta ta farko a gabashin Afrika, an fara gwajin amfani da su. Wannan tagwayen hanyar mota da kamfanonin kasar Sin suka gudanar da aikin gina su, wani muhimmin aiki ne karkashin hadin gwiwar shawarar “ziri daya da hanya daya”. George Karimi, shugaban cibiyar kula da tagwayen hanyar mota ta Nairobi, ya bayyana cewa, aikin gina wannan hanyar mota ta zamani ya samar da guraben ayyukan yi guda 3000 ga mutanen yankin a tsawon lokacin gudanar da ayyukan. A yayin tattaunawa da manema labarai, mutane da dama a Nairobi sun bayyana cewa, aikin gina tagwayen hanyoyin ya kasance a matsayin wani muhimmin aikin da ya daga matsayin samar da guraben ayyukan yi ga al’ummun yankin.

A shekaru sama da biyar da suka gabata, hadin gwiwar shawarar “ziri daya da hanya daya” ta yi matukar karfafa huldar tsakanin mutum da mutum a kasashen dake bin shawarar “ziri daya da hanya daya.” Hilda malecela, wani dan kasar Tanzania mai aikin daukar murya, ya bayyana cewa, idan ana magana kan batun dalilan da suka sanya samun karbuwar wasannin kwaikwayo na talabijin na kasar Sin a kasashen Afrika da dama a shekarun baya bayan nan, Saboda “Sinawa da ’yan Afrika suna da kamanceceniya da juna ta fannin tunani. Al’adun Sinawa suna kama da juna da al’adun kasar Tanzaniya ta fuskoki masu yawa, wanda hakan yake matukar janyo hankali da kuma nuna sha’awar masu kallo ko sauraro."

Ya zuwa ranar 23 ga watan Maris na shekarar 2022, kasar Sin ta sanya hannu kan takardun yarjejeniyoyin hadin gwiwa sama da guda 200, tare da wasu kasashen duniya 149 da kuma kungiyoyin kasa da kasa 32, domin shiga yarjejeniyar gina shawarar “ziri daya da hanya daya.” Hadin gwiwar gina shawarar “ziri daya da hanya daya”, ta samu gagarumar karbuwar daga al’ummun kasa da kasa, kana ta kai wani matsayi a duniya daga matakin shawarar da kasar Sin ta gabatar, inda ta koma yarjejeniyar kasa da kasa. (Ahmad)